25 Agusta 2021 - 10:06
Najeriya : 'Yan Bindiga Sun Kai Hari Makarantar Sojoji NDA

Rahotanni daga Najeriya na cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari a makarantar sojoji ta Nigeria Defence Academy, da ke birnin Kaduna a arewa maso yammacin kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Mai magana da yawun makarantar (NDA) Bashir Jagira, ya bayyana cewa, an kashe wasu jami’an soja biyu, kana an yi awon gaba da guda daya da sanyin safiyar Talatar nan, lokacin da wani gungun ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, suka kai hari a makarantar.

Bashir Jagira, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, ‘yan bindigar sun shiga makarantar ce a ranar Talata da safe, bayan da suka samu muhimman bayanai game da matakan tsaron makarantar.

Hare haren 'Yan bindiga sun zama ruwan dare a yankin arewacin Najeriya musamman jihohin Kaduna da Zamfara da Katsina da Neja, saidai masana harkokin tsaro sun ce basu yi tsammanin lamarin zai kai har zuwa kai hari a makarantar horas da sojojin ba.

342/